Abu huɗu da za ki yi la’akari kafin ci gaba da hulɗa da tsohon saurayinki

Rabuwar masoya na da wahala a soyayya – yanayi ne na rabuwa da mutumin da ba kya ɓoye masa komai a rayuwarki.

Don haka wasu ke ganin ci gaba da hulɗa da juna bayan rabuwar soyayya ya fi komai zafi.

“Ban san mutane masu yawa da suka ci gaba da hulɗa da tsoffin samarinsu bayan rabuwar soyayya ba,» a cewar Olivia Petter, mawallafiyar fitaccen liffafin soyayyar nan mai suna »Millennial Love».

Amma ta ce hakan ba yana nufin ba a samu ba, sai dai ba su da yawa.

Don haka ne ma ta bayar da wasu shawarwari na abubuwan da za ku yi la’akari kafin komawa ci gaba da soyayyar.

Ta lissafo wasu abubuwa huɗu da ta ce ya kamata ki yi la’akari da su wajen ci gaba da hulɗa ko yanke alaƙa da tsohon saurayinki.

1. Yaya ƙarfin soyayyarku kafin rabuwar?

One woman wey get brown hair dey smile, she dey wear blue blouse, sidon for white sofa.

Asalin hoton,Olivia Petter

Bayanan hoto,A cuikin littafin ‘Millennial Love’, Olivia Petter ta dubi yadda soyayyar zamani ke wahalar da samari da ƴanmata.

“Tana da wani saurayi da a baya ta sha romon soyayya da shi, amma daga bara suka koma mutunci bayan rabuwar soyayyar,» kamar yadda Olivia ta shida wa BBC.

Ta ce “Shaƙuwar da muka yi a baya baya ta taimaka wajen yafewa juna tare da zama sabbin abokai a yanzu ba tare da wata damuwa kan abin da ya faru a baya ba,».

Deja un comentario